Cikin wani taron ba da tallafin jin kai ga Yemen, da aka yi jiya a Geneva, Antonio Guterres ya bayyana cewa, ya kamata masu ruwa da tsaki a rikicin Yemen, su mutunta dokar kasa da kasa, su kuma hada kai da MDD don kiyaye fararen hula da manyan ababen more rayuwa. A cewarsa, yin shawarwari tsakaninsu, ita ce hanya daya tilo ta magance rikicin da ake fuskanta a kasar.
Rahotanni na cewa, taron ya samu halartar wakilai kimanin 300 daga kasashe ko yankuna 60 da kungiyoyin kasa da kasa da kuma masu zaman kansu, inda aka ba da tallafin da ya kai dala biliyan 2. Ban da wannan kuma, bisa kididdigar da MDD take yi, yawan kudin tallafin jin kai da Yemen ke bukata cikin shekarar 2018 ya kai dala biliyan 3. (Amin Xu )