Wu Haitao wanda ya yi wannan tsokaci a zaman kwamitin tsaro na MDD game da yanayin da ake ciki a gabas ta tsakiya, ya ce Sin ta yi matukar damuwa game da amfani da makamai masu guba kan fararen hula a kasar Syria.
A baya bayan nan ma dai akwai zargin sake amfani da wani nau'in guba a kasar Syria, matakin da a cewar Mr. Wu ke da matukar ta da hankali. Ya kuma kara da cewa, akwai bukatar gudanar da sahihin bincike, domin gano gaskiyar al'amarin da ya auku, tare da daukar matakan kare faruwar hakan a nan gaba.
Ya ce ya dace dukkanin sassa masu ruwa da tsaki a wannan lamari, su yi hadin gwiwa da kwamitin tsaro na MDD, da hukumar dake yaki da yaduwar makamai masu guba ta kasa da kasa ko OPCW a takaice, wajen lalubo hanyoyin dakile amfani da irin wadannan makamai. (Saminu Hassan)