in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Kudaden da ake kashewa a fannin bincike da samar da ci gaba sun karu cikin shekaru 5
2018-01-10 11:10:31 cri
Ministan ma'aikatar kimiyya da fasaha a kasar Sin Wan Gang, ya ce kasarsa ta samu babban ci gaba a fannin bunkasa sashen bincike da samar da ci gaba a tsawon shekaru biyar din da suka gabata, sakamakon karin kudade da ake kashewa a fannin.

Da yake tsokaci game da hakan yayin wani taron karawa juna sani, Mr. Wan ya ce yawan kudaden da aka kashe cikin shekarar 2017 a wannan fanni, sun kai kimanin kudin Sin Yuan tiriliyan 1.76, adadin da ya haura na shekarar 2012 da kusan kaso 70.9 bisa dari.

Ministan ya kara da cewa, adadin kudin da aka kashe a baran, sun kai kaso 2.15 bisa dari na daukacin ma'aunin tattalin arzikin kasar Sin na GDP, wanda ya yi kusa da matsakaicin adadin kaso 2.1 bisa dari, da kasashen dake karkashin kungiyar tarayyar Turai 15 suka kashe a shekarar.

Jami'in ya kuma kara da cewa, kamfanonin fasahohi 136,000 ne suka samar da sama da rabin kudaden bincike da samar da ci gaba da aka gudanar a baran.

A bangaren rubuce rubuce kuwa, minista Wan ya ce masu bincike na kasar Sin, sun gabatar da makaloli da suka kai matsayi na biyu da yawa a duniya baki daya, yayin da yawan makalolin da ake kafa hujja da su daga kasar ta Sin, suka haura na kasashen Jamus da Birtaniya, suka kuma zamo na biyu a duniya ta fuskar yawa a shekarar ta 2017.

A daya hannun kuma, takardun neman izinin mallakar ikon fasaha da aka nema, da wadanda aka bayar a kasar ta Sin a shekarar ta bara, sun haura na dukkanin sauran kasashen duniya yawa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China