Hukumar zaben kasar ta sanarwa dukkan 'yan kasar dake zaune a kasashen ketare cewa ya zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2018, an rufe aikin rejistar masu kada kuri'ar dake zaune a kasashen waje, inda kawo yanzu hukumar ta yi rejistar kimanin mutane 6630.
Sanarwar tace an yi rejistar ne ta hanyar ofisoshin jakadancin kasar Libyan dake kasashen waje, wanda a halin yanzu an rufe aikin.
Hukumar tace, an kawo karshen aiki rejistar ne wanda aka fara shi a ranar 6 ga watan Disambar shekarar 2017, inda hukumar ta taya murna ga dukkan masu zabe dake kishin kasarsu wajen aza tubalin tabbatar da zaman lafiya da cigaban kasar.