in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na samar da tallafi ga mata 'yan gudun hijira sama da 8,000 a Libya
2018-03-31 12:43:22 cri

Hukumomin MDD da suka hada da na kula da 'yan gudun hijira UNHCR da asusun kula da yawan al'umma UNFPA, sun tallafawa mata 'yan gudun hijira sama da 8,000 a fadin Libya.

Wata sanarwa da shirin tallafi na MDD dake aiki a Libya ya fitar, ta ce domin kai dauki ga karuwar bukatun mata 'yan gudun hijira masu rauni a fadin Libya, hukumomin UNHCR da UNFPA da tallafin kudi daga Jamus, yanzu haka, na rarraba kayakin tsafta da na bukata a wurare daban-daban guda 16, na yankunan Tripoli da Misrata da Sabha da Nafusa da Mountains da Bani Walid da Janzour da Ubari da kuma Murzaq.

Sanarwar ta ruwaito cewa, mata da 'yan mata 'yan gudun hijira, su ne suka fi rauni a Libya, inda aka yi kiyasin mutane 500,000 sun yi gudun hijira ko kuma sun koma gida bayan sun yi gudun hijira.

Shirin tallafin ya ce hukumomin za su ci gaba da mara baya ga karfafawa mata da kare 'yan mata da mata 'yan gudun hijira a Libya, ta yadda za su taimaka musu shiga a dama da su ciki harkokin kungiyoyin al'umma tare da tabbatar da ana saurarensu.

Da farko, shirin na MDD ya kaddamar da wani shiri na kai daukin jin kai a Libya, wanda ke neman samar da dala miliyan 313 domin taimakawa al'ummar Libya sama da miliyan 1. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China