in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Adadin sayayyar kayayyaki zai karu da kaso 10 bisa dari a 2018
2018-02-07 09:14:16 cri

Wani rahoton bincike da cibiyar bunkasa harkokin cinikayyar kasa da kasa ta kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, adadin sayayyar kayayyaki a cikin kasar Sin zai karu a shekarar nan ta bana da kusan kaso 10 bisa dari, ta yadda kudaden da za a kashe a fannin za su kai kudin kasar sama da Yuan tiriliyan 40, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 6.38.

Rahoton wanda aka fitar a jiya Talata, ya nuna irin tasiri da fasahohin sadarwa na zamani ke kara yi a fannin bunkasa hada hadar saye da sayarwa, a gabar da al'ummar Sinawa ke kara nuna sha'awar su ga ta sayen hajoji masu nagarta.

Har ila yau idan aka kwatanta da shekarar 2017 da ta gabata, cinikayyar hajoji a kasar Sin ta fadada da kaso 10.2 bisa dari, adadin da ya haura na shekarar bara bisa kudi sama da tiriliyan 36.

Bugu da kari, rahoton ya bayyana sashen saye da sayarwar a matsayin wanda zai samar da sama da kaso 60 bisa dari na daukacin GDPn kasar, yayin da kuma gibin dake tsakanin birane da yankunan karkara a fannin sayayya ke kara raguwa.

Daya daga masana na cibiyar ta CCPIT Zhao Ping ya bayyana cewa, hidimomi ta yanar gizo na kan gaba wajen fadada hada hadar cinikayya a wannan lokaci.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China