in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a kafa wani sabon tsarin hadin gwiwar Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki, in ji masana
2018-03-01 10:53:45 cri

Jiya Laraba, wasu shahararrun masana Sinawa sun bayyana a birnin Beijing cewa, ba zai yiyuwa ba yakin ciniki ya barke a tsakanin Sin da Amurka daga dukkan fannoni, amma akwai sabani a tsakaninsu a wasu sana'o'i. Don haka sun yi kira ga bangarorin biyu da su inganta hadin kansu, don kafa wani sabon tsarin hadin kai ta fuskar tattalin arziki tsakaninsu.

Masanan sun yi wannan furuci ne don mayar da martani kan yadda kasar Amurka ta dauki matakan ba da kariya kan cinikayyarta ba kamar yadda ya kamata ba a kwanakin baya, da yawan zuzuta labarai kan yadda kasar Sin ke kawo barazana ga saura, musamman ma karbar kudin haraji masu dimbin yawa ga injunan wanke tufafi da aluminium foil da kasar Sin ta sayarwa Amurka bisa hujjar wai hana sayar da kayayyaki masu yawa cikin farashi mai rahusa da hana samun rangwame daga gwamnati, lamarin da ya jawo hankalin sassa daban daban.

A yayin taron wata-wata na karawa juna sani ta fuskar tattalin arziki da aka kira jiya a cibiyar cudanyar tattalin arziki ta kasa da kasa ta kasar Sin, masana Sinawa da dama suna ganin cewa, ban da gibin kudi wajen yin cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, da damuwar da Amurka ke nunawa kan farfadowar kasar Sin, da kuma zaben majalisun dokoki da za a yi a Amurka, ra'ayin bada kariyar cinikayya da nuna banbanci tsakanin mawadata da matalauta da Amurka ke dauka, su ne dalilan da suka haddasa wannan yanayin da ake ciki a yanzu. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China