in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi na jagorantar Sin wajen gina yanar gizo mai cikakkiyar kariya
2018-04-19 20:08:45 cri

Ya zuwa yanzu kasar Sin na samun ci gaba cikin sauri a fannin amfani, da kuma bunkasar sha'anin sadarwa ta yanar gizo. A birane, al'ummar kasar na amfani da woyoyin salula wajen yin sayayya a shaguna, da odar abinci, da kiran motar haya, da biyan hidimomin yau da kullum da dai sauran su.

Kididdiga ta nuna cewa, kasar Sin na da masu amfani da yanar gizo miliyan 700, da shafukan yanar gizo sama da miliyan 4, tana kuma da kasuwar tsarin amfani da yanar gizo mafi karfi ta 4G, mafi girma a duniya.

Cikin wani jawabi da ya gabatar, yayin taron tsaron yanar gizo da tattara bayanai a 19 ga watan Afirilu na shekarar 2016, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce ya kamata a kara azama wajen fadada hidimomin da ake samarwa ta yanar gizo ga karin mutane, su kuma zama masu araha, ta yadda al'ummar kasar a ko ina za su iya cin gajiyar hakan.

Shugaba Xi ya ce tattara manyan bayanai, shi ne aiki mai muhimmanci na gaba a fannin samar da ci gaban fannin. Don haka ya umarci masu ruwa da tsaki a kasar da su kara nazari a fannin habaka samar da manyan bayanai, tare da hade hakan da ci gaban rayuwar al'umma.

Daga nan sai ya yi kira ga dukkanin sassa da su bada gudummawa, ta mayar da yanar gizo ta zamo mai amfani ga daukacin bil Adama, ta kuma zamo mai nagarta da karko, da cikakken tsaro.

Ya ce ci gaban Sin, ta fannin amfani da yanar gizo na da tasiri wajen gamsar da al'umma game da nasarorin da kasar su ke samu, kana hanya ce ta zaburar da ci gaba da ake fatan kasar za ta samu cikin hanzari.

Karkashin jagorancin JKS da tunanin shugaba Xi a matsayin jigo, Sin ta karfafa sassan amfani da yanar gizo, wanda kuma hakan ya yi tasiri ga ci bunkasar kasar daga dukkanin fannoni.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China