Shugaban na Sin ya bayyana hakan ne a Juma'ar nan, a jawabin da ya gabatar na bikin cikar lardin na Hainan, da yankin raya tattalin arziki na musamman na Hainan shekaru 30 da kafuwa.
Ya ce Sin na maraba da daukacin kasashen duniya, da su shigo domin cin gajiyar damammakin samar da ci gaba, da sakamakon sauye sauye da kasar ke aiwatarwa.