in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya buga waya ga shugaban kasar Turkiya
2018-04-19 21:24:32 cri
A yau ranar 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya buga waya ga takwaransa na kasar Turkiya Recep Tayyip Erdoğan bisa gayyatar da aka yi masa.

Xi Jinping ya bayyana matsayin kasar Sin kan batun kasar Syria, ya jaddada cewa, ya kamata bangarori daban daban da abin ya shafa su gudanar da aiki bisa tsarin dokokin kasa da kasa, da bin ka'idojin tsarin mulkin MDD, da girmama ikon mallaka da 'yancin kai, da cikakken yankunan kasa da kasa.

A nasa bangare, Erdoğan ya bayyana cewa, kasar Turkiya ta dora muhimmanci kan tasirin da kasar Sin ta yiwa batun kasar Syria ta hanyar siyasa, tana kuma fatan kara mu'amala tare da kasar Sin kan batutuwa masu nasaba da hakan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China