in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya gana da shugaban dandalin WEF
2018-04-16 19:25:01 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban dandalin raya tattalin arziki na duniya WEF Klaus Schwab, a babban dakin taruwar jama'a dake nan birnin Beijing.

Da yake tsokaci yayin tattaunawar ta su, shugaba Xi ya ce da yake hadin gwiwar Sin da dandalin na WEF ya dace da manufofin kasar Sin na aiwatar da gyare gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, kamata ya yi sassan biyu su kara azama wajen tafiya tare da zamani, su karfafa hadin kai, ta yadda za su cimma wani sabon zarafi na bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya, su kuma lalubo managartan hanyoyin warware kalubale daban daban dake addabar duniya baki daya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China