Jaridar Herald mallakar gwamnatin kasar ta wallafa wani rahoto a shafinta na yanar gizo dake cewa, bisa ga jerin sunayen masu sanya idon da kasar ta gayyata, wanda ma'aikatar harkokin waje da hada hadar cinikin kasa da kasa ta kasar ta fitar ya nuna cewa, akwai wasu hukumomi na shiyya da nahiyoyi kimanin 15 wadanda kasar ta gayyata don su sanya ido a zaben kasar.
Daga cikin wadanda kasar ta gayyata har da kungiyar tarayyar Turai da kasar Amurka, wadanda suka jima ba su halarci kasar don sanya ido a zaben ba tun a shekarar 2002, a lokacin da dangantakarsu ta yi tsami da kasar bisa zargin da ake yiwa Zimbabwe na take hakkin bil adama.
Goron gayyatar da aka baiwa masu sanya ido daga kasashen waje ya zo ne a daidai lokacin da kasar Zimbabwen ke ci gaba da fadi tashin ganin an gudanar da sahihin zabe mai tsabta wanda shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya ayyana hakan.
A watan jiya ma, wata tawaga daga al'ummar raya ci gaban kasashen kudancin Afrika da wata tawaga daga kungiyar tarayyar Turai sun ziyarci kasar ta Zimbabwe a mabanbantan lokuta, domin duba irin shirye-shiryen da kasar ke yi wajen tunkarar zaben. (Ahmad Fagam)