in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gayyaci Zimbabwe taron kolin Commonwealth a London
2018-04-16 10:22:06 cri
Kafafen yada labaran kasar Zimbabwe sun bada rahoton cewa an gayyaci kasar don halartar taron kolin shugabannin kasashen renon Ingila wato Commonwealth wanda za'a fara a yau Litinin a birnin London kuma za a kammala shi a ranar Lahadi mai zuwa, matakin da ake ganin ya kawo karshen zaman tankiya tsakanin kasar ta Zimbabwe da Birtaniya.

To sai dai duk da haka, kasar za ta kasance a matsayin 'yar kallo ce kuma ba za ta iya gabatar da wata mahawara ba a lokacin taron.

Tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ne ya tsame kasar Zimbabwe daga cikin kungiyar ta Commonwealth a shekarar 2003, bayan da aka samu sabanin fahimta a game da wasu batutuwa da suka shafi sha'anin shugabanci.

Da yake zantawa da kafar yada labarai ta Sunday Mail, sakataren harkokin wajen da cinikayyar kasa da kasa ta Zimbabwe Joey Bimha, ya ce goron gayyatar da aka ba ta zuwa taron na Commonwealth alama ce dake nuna Zimbabwe tana da sha'awar sake shiga kungiyar.

Ya ce ministan harkokin wajen kasar Sibusiso Moyo zai halarci taron kolin.

A cewarsa ministan ya samu goron gayyata ne daga takwaransa na kasar Birtaniya inda ya bukace shi da ya kai ziyarar. Kuma zai halarci taron, sai dai ba zai shiga a dama da shi ba.

Ya kara da cewa, ba za su samu damar gabatar da wani kuduri a taron kolin ba, kasancewa ba sa daga cikin mahalarta taron. Amma ya ce alamu sun nuna cewa shirye shiryen sake komawa kasar cikin kungiyar yana aiki matuka. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China