in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mnangagwa: Ziyarata zuwa kasar Sin ta cimma nasara sosai
2018-04-08 11:27:10 cri
Da safiyar jiya Asaba 7 ga wata, shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, wanda ya kammala ziyararsa a kasar Sin bada dadewa ba ya komo Harare hedkwatar kasar Zimbabwe. Inda ya shedawa manema labarai a filin saukar jiragen sama cewa, ziyararsa a wannan karo ta samu nasara mai armashi. Ya ce, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta shiga wani sabon matsayi na hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. Banda wannan kuma, hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki tsakaninsu zai kara samun ci gaba. A nata bangare kuwa Zimbabwe zata sa kaimi ga aiwatar da kyawawan sakamakon da aka samu a wannan ziyara.

Daga bisani kuma, ministocin dake rufawa shugaban baya a yayin wannan ziyara sun martaba ziyarar ta wannan karo. Ministan kudi Patrick Chinamasa ya bayyana cewa, za a gudanar da ayyukan gina manyan ababen more rayuwa guda uku dake karkashin taimakon kamfanonin kasar Sin cikin hanzari.

Haka zalika, ministan harkokin waje Simon Kaya Moyo ya ce, a wannan karo sun kai ziyara a makarantar horas da jami'an jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, abin da ya zama zarafi mai kyau gare shi wajen fahimtar muhimmancin binciken wata ka'ida ko tsare-tsare bisa hanyar gudanar da shi, lamarin da ya kara bude idonsa wajen yadda za a gudanar da ayyukan kasa. A ganinsa, Zimbabwe zata canja bisa wannan dabara. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China