Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya bayyana cewa batun zaman lafiya ya kasance wani batu dake fuskantar babbar barazana a kasashen Afrika, musamma idan aka yi la'akari da matsalolin da suka hada da yawaitar ayyukan ta'addanci, tashe tashen hankula, talauci da matsalar sauyin yanayi.
Paul Biya ya yi Allah wadai da karuwar tashe tashen hankula da ake samu a nahiyar Afrika, da Asiya, da Latin Amurka da kuma yankin gabas ta tsakiya, wadanda ke haifar da tabarbarewar al'amurra da jefa al'umma cikin matsanancin hali. Ya ce jamhuriayr Kamaru ta karba kuma tana cigaba da karbar bakuncin dubun dubatar 'yan gudun hijira daga jamhuriyar Afrika ta tsakiya da kuma Najeriya.
Biya, ya bukaci dukkanin kasashen duniya su yi aiki tare domin tabbatar da zaman lafiyar duniya, kana ya bukaci kasashen duniyar dasu dauki wannan sako na Afrika da muhimmancin gaske.
Da yake karin haske game da kalaman na mista Biya, shugaban jamhuriyar Afrika ta tsakiya Faustin-Archange Touadera, ya nanata muhimmancin aza tubulin tabbatar da zaman lafiya da kuma warware duk wata takaddama ta hanyar tattaunawar sulhu.