Da yake mayar da martani a jiya Lahadi, game da tsokacin da ake kan sabon tsarin majalisar dokokin kasar na rabon filaye, Lindiwe Sisulu, ya ce babu bukatar a tada hankali ko fargaba, yana mai cewa dole ne a mutunta tsare-tsaren majalisar.
Ya ce al'ummomin kasashen waje sun taka muhimmiyar rawa wajen yaki da wariyar launin fata da dukkan wasu banbance-banbancen da ya kunsa, Inda ya ce suna bukatar su ci gaba da mara musu baya ga kokarin da suke na kawar da wariyar launin fata.
A baya-bayan nan ne majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin gyara wani bangare na dokar da ta bada damar kwace filaye ba tare da biyan diyya ba. (Fa'iza Mustapha)