Hukumar zartaswar kungiyar ta tabbatar da hakan a makon da ya gabata, matakin da kuma ya biyo bayan amincewar da wasu kasashe mambobin kungiyar su 44 suka yi, da kudurin nan na kafa yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar ko CFTA a takaice.
Wata sanarwa da sakatariyar AUn ta fitar a Alhamis din nan, ta bayyana wannan mataki, a matsayin shaidar dake nusar da duniya ikon da nahiyar Afirka ke da shi na dunkulewa waje guda, da kuma magana da yawu daya.(Saminu Alhassan)