in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da 'yan gabashin Afrika 110 ne suka isa Kenya bayan Amurka ta tasa keyarsu
2018-03-31 13:13:35 cri

Sama da 'yan kasashen Kenya da Somalia da Sudan ta kudu 100 da aka mai da gida daga Amurka ne suka isa birnin Nairobin Kenya a jiya Jumma'a.

'Yan sanda da jami'an kula da shige da fice a filin jirgin saman kasa da kasa na Jomo Kenyatta, sun ce 'yan asalin kasar Kenya 20 na daga cikin mutanen da suka sauka a filin jirgin da safiyar jiya Jumma'a.

Wani jami'in dan sanda, ya ce jirgin kamfanin Omni Internatinal na Amurka ne ya sauke mutanen da misalin karfe 10 da wasu mintoci na safiyar jiya.

Jami'an sun ce dama ana sa ran zuwan mutanen, la'akari da aikin dake gudana a Amurka na zakulo wadanda ke kasar ba bisa ka'ida ba.

Dan sandan ya ce an kyale 'yan asalin kasar Kenya su zarce gida, yayin da jirgin ya wuce da 'yan asalin Somalia 70 zuwa Mogadishu, bayan sanya 'yan kasar Sudan ta kudu 24 cikin jirgin da zai tafi Juba.

Wannan shi ne kashi na baya-bayan nan da Amurka ta tasa keyarsu cikin shekaru 2 na mulkin Donald Trump.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China