in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Kenya: Amurka za ta lahanta moriyar kanta
2018-04-10 13:40:06 cri
Henry Rotich, ministan kudi da tsare-tsare na kasar Kenya, ya furta a kwanakin baya cewa, idan kasar Amurka ta ci gaba da daukar manufarta ta kariyar ciniki, to, a karshe,za ta lahanta moriyar kanta, gami da yin mummunan tasiri ga kasuwannin duniya.

Yayin da yake hira da wakilin CRI, mista Rotich ya nuna damuwa kan jerin sakamakon da za a iya samu bisa tsananta rikicin cinikin da ya abku tsakanin kasar Amurka da kasar Sin. A cewarsa, tsayawa kan manufar bude kofa ga daukacin duniya bisa tsarin kungiyar cinikin duniya ta WTO, zai bada damar aiwatar da wani tsarin da ya shafi bangarori daban daban a kasashen dake nahiyar Asiya da ta Afirka, don kau da shingen ciniki da harajin kwastam a wadannan kasashe.

Jami'in ya kara da cewa, bude kofa shi ne dalilin da ya sa ake samun karfi wajen takara da sauran kasashe, kana idan babu irin wannan takara, matakan da aka dauka na hana wasu kasashe gudanar da ciniki za su lahanta moriyar kasashen da suka dau matakan. A cewarsa, duniyarmu ta yanzu ta sha bamban da yadda duniya take a baya. A zamanin yanzu, kowace kasa na kokarin raya tattalin arziki. Amma a ra'ayinsa, kariyar ciniki za ta yi illa ga ci gaban tattalin arziki, lamarin da zai hana cikar burin da aka sanya gaba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China