in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin kasar Sin ya ce aikin shimfida layin dogo na kasar Kenya ba zai yi barazana ga gidan adana namun dajin kasar ba
2018-04-13 14:05:48 cri
Kamfanin kasar Sin dake aikin tsawaita layin dogo na zamani daga birnin Nairobin Kenya zuwa Naivasha, ya ce aikin ba zai yi tarnaki ga namun daji da sauran muhallin halittu dake kusa da shi ba.

Kakakin kamfanin ofishin dake aikin a Kenya Steve Zhao, ya ce za a kiyaye dokokin muhalli a yayin ginin kashi na biyu na layin dogon, wanda ya ratsa ta gidan adana namun daji da wasu muhimman yankunan raya halittu.

Steve Zhao, ya bayyana cewa, ginin gadar a kan hanyar da a baya kungiyoyin da ke rajin kare muhalli ke adawa da shi, ya samu sahalewar hukumar kula da namun daji na kasar da hukumar kiyaye muhalli, tun da ba shi da wata barazana ga dabbobi da tsirrai.

Ya shaidawa Xinhua cewa, sun kuduri aniyar kiyaye shawarwarin hukumomin a kokarinsu na takaita yin illa ga tsirrai da dabbobi a yankin.

Game da yadda za a shirya ginin kuwa, ya ce za a yi aikin kebe shingen gidan namun dajin mai wutar lantarki da yankin ginshikin ginin cikin kashi biyu, don tabbatar da dabbobi sun yi zirga-zirga ba tare da wata matsala ba yayin aikin ginin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China