in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutum guda ya mutu yayin arangamar 'yan sanda da masu zanga-zangar a helkwatar Najeriya
2018-04-17 09:19:42 cri
Shedun gani da ido da wata majiya ta cikin gida sun tabbatar da mutuwar mutum gudu wanda aka harba a lokacin da 'yan sanda ke kokarin tarwatsa gungun masu zanga-zanga a jiya Litinin a Abuja babban birnin Najeriya.

Zanga-zangar da mabiya Shi'a ke yi na neman a sako jagoransu a Najeriya ta rikide zuwa tashin hankali bayan da masu zanga-zangar suka afkawa tawagar jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma.

Jami'an 'yan sandan sun hana masu zanga zangar shiga dandalin Unity Fountain dake yankin Maitama a Abuja, inda masu zanga zangar suka taba yin dandazo a yankin a lokutan baya.

A ranar Juma'a hukumomin 'yan sandan birnin tarayyar kasar suka haramtawa masu zanga zangar shiga dandalin na Unity Fountain, sakamakon dalilai na tsaro.

Su dai mabiya Shi'a, wadanda aka fi sani da kungiyar 'yan uwa musulmi ta Najeriya, suna zanga-zangar neman a saki shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky, wanda 'yan sanda ke tsare da shi tun a watan Disambar shekarar 2015, tun bayan wata arangama a tsakanin mabiya kungiyar da sojojin Najeriya a jihar Kaduna dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Mabiya Shi'ar sun yi gangami a titunan birnin Abuja a ranar Juma'ar da ta gabata, domin matsawa gwamnati lamba don ta sako shugabansu El-Zakzaky. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China