Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, babban birnin kasar, Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin kasar (CBN) ya ce, makomar tattalin arzikin kasar na shekarar nan ta 2018 ya kasance cikin kyakkyawan yanayi amma hakan zai ta'allaka ne kan amincewa da kuma aiwatar da kasafin kudin kasar na shekarar 2018 a kan lokaci.
Emefiele, wanda ya gabatar da jawabi a karshen taron kwamitin tsara al'amurran kudin kasar (MPC) na shekarar 2018, ya kara da cewa, ci gaban da tattalin arzikin kasar ya samu ya samo asali ne daga kyautatuwar al'amurran tsaro da aka samu a kasar, da daidaituwar kasuwar masuyar kudaden kasar, da kuma ingancin farashin albarkatun danyen mai a kasuwar duniya.
Ya ce mambobin kwamitin na MPC sun kada kuri'ar amincewa da ci gaba da tafiyar da tsarin kudaden kasar kan matakin da ake amfani da shi a halin yanzu da ma sauran batutuwa da suka shafi harkokin kudade a kasar.
A cewarsa, kwamitin yana da ra'ayin cewa tsaurara matakan zai yi tasiri kan tsarin kudaden kasar game da hawa-hawar farashin kayayyaki wanda kuma zai iya shafar yadda kudaden kasar ke gudana da kuma daidaita kasuwar musayar kudade a kasar. (Ahmad Fagam)