A cewar UNICEF, tun bayan da rikicin Boko Haram ya barke a arewa maso gabashin Nijeriya kusan shekaru 9 da suka gabata, a kalla malamai 2,295 aka kashe yayin da aka lalata makarantu sama da 1,400, inda ya ce har yanzu ba a bude galibin makarantun ba saboda yadda hare-haren suka lalata su ko kuma saboda rashin tsaro da har yanzu ake fama da shi.
Batun na sace yara ya kara jan hankalin al'umma ne a lokacin da aka sace 'yan mata 276 daga sakandaren garin Chibok a shekarar 2014.
Shekaru 4 ke nan tun bayan aukuwar al'amarin, amma har yanzu ba a kai ga dawo da sama da 100 daga cikinsu ga iyalansu ba.
Har ila yau, asusun ya ce harin baya-bayan nan da aka kai Sakandaren garin Dapchi, inda 'yan mata 5 suka rasa rayukansu alamu ne dake nuna cewa a wurare kalilan ne kawai yara ke da tabbacin tsaro a yankin arewa maso gabashin Nijeriya
Asunsun, ya lashi takobin goyon bayan hukumomin Nijeriya, wadanda suka jajirce wajen tabbatar da tsaro a makarantu ta hanyar ba su kariya daga rikice-rikice. (Fa'iza Mustapha)