in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan al'ummar Najeriya ya kai miliyan 198
2018-04-12 09:45:39 cri
Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika, ta sanar cewa, yawan jama'arta a halin yanzu ya kai miliyan 198, yayin da ake samun karuwar mutanen dake zaune a biranen kasar da kashi 6.5 bisa 100.

A wata sanarwa da hukumar kidayar jama'a ta kasar (NPC) ta fitar ta bayyana cewa, nau'in mutanen dake kaura zuwa birane galibi matasa ne da mata dake shekarun haihuwa da renon 'yaya da kuma wadanda suke kan ganiyar shekarun aiki.

Hasashen baya bayan nan da hukumar kula da yawan al'umma ta duniya ta yi ya nuna cewa, nan da shekarar 2050, Najeriya zata kasance kasa ta uku mafi yawan jama'a a duniya.

Ya zuwa wancan lokacin, kashi 70 bisa 100 na yawan al'ummar Najeriyar za su kasance mazauna birane ne, kamar yadda hukumar kididdiga ta duniya ta yi hasashe.

NPC ta ce, yawan al'ummar Najeriya ya karu daga kashi 17.3 bisa 100 a shekarar 1967 zuwa kashi 49.4 bisa 100 a shekarar 2017.

Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta sanar cewa, a halin yanzu, manyan biranen kasar suna da yawan masu fama da fatara da rashin aiki yi, kuma adadin marasa aikin yin sun kai kashi 18.4 bisa 100.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China