in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun hallaka wasu 'yan bindiga 21 a Zamfara
2018-04-06 12:00:15 cri
Rahotanni daga jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya, na cewa dakarun sojojin Najeriya sun hallaka wasu masu dauke da makamai 21, kana wasu sojoji biyu sun rasa rayukan su, yayin wani bata-kashi da suka gwabza a ranar Laraba.

Kakakin rundunar sojin kasar Texas Chukwu, ya ce 'yan bindigar ne suka yiwa sojojin kwantan-bauna a yankin Anka dake jihar ta Zamfara, inda kuma nan take sojojin suka bude musu wuta.

Texas Chukwu wanda ya shaidawa manema labarai aukuwar wannan lamari jiya a birnin Gusau, fadar mulkin jihar ta Zamfara, ya kuma ce da yawa daga masu dauke da makaman sun gudu dauke da raunukan bindiga a jikin su.

Wani ganau ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, 'yan bindigar sun yiwa sojojin da aka tura domin murkushe 'yan fashin shanu da sauran 'yan ta'adda a jihar kofar rago, amma sai sojojin suka ci lagon su.

A cikin watan jiya ne dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin tura karin sojoji jihar ta Zamfara, domin murkushe ayyukan ta'addanci da ake alakantawa da barayin shanu, wanda daga bara zuwa wannan shekara ya yi sanadiyar kisan fararen hula masu tarin yawa a jihar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China