in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta damke mutane 89 bisa zarginsu da safarar muggan kwayoyi a jaha mai arzikin mai
2018-04-12 09:54:58 cri
Gwamnatin Najeriya ta sanar a ranar Laraba cewa, a rubu'in farko na wannan shekarar ta samu nasarar cafke mutane 89 da take zarginsu da hannu a safarar miyagun kwayoyi a jahar Bayelsa mai arzikin mai dake shiyyar kudancin kasar.

Kakakin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar NDLEA a Yenagoa, babban birnin jahar ta Bayelsa, Ikenna Osakwe, ya sanar cewa, hukumar ta kwace nau'in kayan sa maye da nauyinsu ya kai kilogram 73.779 a jahar, ya kara da cewa, daga cikin adadin mutanen da hukumar ta damke, 68 maza ne yayin 21 kuma mata ne.

Yace daga cikin kididdigar miyagun kwayoyin da hukumar ta kama, tabar wiwi itace mafi yawa wanda nauyinta ya kai kilogram 62.093.

Osakwe ya bayyana damuwa game da karuwar miyagun laifuka a jahar, da suka hada da hallaka rayukan jama'a, yin garkuwa, tsafe-tsafe, fashi da makami da sace sace, duka wadan nan muggan laifukan suna da nasaba da karuwar ta'ammali da miyagun kwayoyin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China