Shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin na koli na JKS, kuma shugaban kwamitin koli na sojin kasar Sin, ya bayyana hakan ne a juma'ar nan, a jawabin da ya gabatar na bikin cikar lardin na Hainan, da yankin tattalin arziki na musamman na Hainan shekaru 30 da kafuwa.
Ya ce ya kamata yankunan raya tattalin arziki na musamman, su kasance kan manufar da aka kafa su, tare da amfani da matsayin da aka ba su, domin cimma burin da aka sanya gaba. Kaza lika shugaban na Sin ya bukace su da su ci gaba da zama mafari na aiwatar da sauye sauye, da kara bude kofa ga ketare.