
Da sanyin safiyar Alhamis din nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya duba tsarin ayyukan rundunar sojin ruwan dake tekun kudancin kasar ta Sin, inda ya bayyana cewa, ba wani lokaci da ya fi dacewa a karfafa rundunar sojin ruwan Sin sama da wannan lokaci.
Shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kuma shugaban kwamitin sojojin kasar ta Sin, ya ja hankalin dukkanin sassan masu ruwa da tsaki, da su kara azama wajen samar da rundunar sojin ruwa mafi karfi a duniya. (Saminu)