Xi Jinping: Kwamitin koli na JKS ya goyi bayan zurfafa gyare-gyare da lardin Hainan ke aiwatarwa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar wato JKS na matukar goyon bayan ayyukan zurfafa gyare gyare, da bude kofa da mahukuntan lardin Hainan ke gudanarwa, yana mai fatan lardin zai kokarta ya zama misali ta fannin raya salon mulkin gurguzu mai halayyar musamman na kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki.
Shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin na koli na JKS, kuma shugaban kwamitin koli na sojin kasar Sin, ya bayyana hakan ne a juma'ar nan, a jawabin da ya gabatar na bikin cikar lardin na Hainan, da yankin tattalin arziki na musamman na Hainan shekaru 30 da kafuwa.