A sakon da ya aike, Xi ya ce ya yi matukar kaduwa bayan da ya samu labarin hadarin jirgin saman, wanda ya yi sanadiyyar hallaka rayuka masu yawan gaske.
Ya ce a madadin gwamnatin kasar Sin da al'ummar Sinawa, da kuma shi kansa, Xi yana mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su.
Shi ma firaiministan kasar Sin Li Keqiang ya aike da sakon ta'aziyyar ga takwaransa na kasar Algeria, Ahmed Ouyahia, bisa hadarin jirgin saman sojojin kasar da ya afku.
Da safiyar ranar Laraba ne dai wani jirgin saman sojin kasar ta Algeria ya yi hadari a lardin Blida, mai tazarar kilomita 30 dake shiyyar kudu maso yammacin Algiers babban birnin kasar, inda ya hallaka mutane 257 dake cikin jirgin, ciki har da matukan jirgin su 10.
Ma'aikatar tsaron kasar Algeria ta tabbatar da cewa, wannan shi ne hadari mafi muni a tarihin kasar.(Ahmad Fagam)