Kasar Kenya dake gabashin Afirka, tana da albarkatun yawon shakatawa. A yayin da ake kara yin mu'amalar al'adu a tsakaninta da kasar Sin. Yawan Sinawa dake zuwa kasar Kenya don yawon shakatawa yana ta karuwa, wato ya kai dubu 69 a shekarar 2017, wanda ya kai kashi 5.5 cikin dari bisa yawan dukkan mutanen kasashen waje da suka je kasar Kenya yawon shakatawa.
Wang Xuezheng ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, kafa kungiyar yawon shakatawa ta Sinawa dake zaune a kasar Kenya tana da babbar ma'ana wajen sa ido kan yadda kamfanonin yawon shakatawa masu jarin Sinawa dake kasar Kenya suke tafiyar da harkokinsu, da samar da hidima ga masu yawon shakatawa na kasar Sin, da kuma inganta hadin gwiwa a tsakanin Sin da Kenya a fannin yawon shakatawa. Ana fatan kungiyar za ta inganta karfin sa ido kan kamfanonin da kare moriyar masu yawon shakatawa na kasar Sin bisa doka yadda ya kamata. (Zainab)