in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci kasashen Afrika da su rika samarwa al'umma makamashin gas na girki
2018-04-13 14:02:57 cri

MDD ta bukaci gwamnatocin Afrika, da su rika samarwa al'ummominsu marasa karfi makamashin gas na girki, domin ya maye gurbin amfani da icce.

Sakatariyar zaratarwa ta dandalin yarjejeniyar sauyin yanayi na MDD Patricia Espinosa, ta ce a yanzu, an rage amfani da makamashi mai illa, saboda samun makamshi mai tsafta a nahiyar.

Sakatariyar ta ce suna son cimma burinsu kan lokaci ya cimma musu, a don haka, akwai bukatar rungumar wasu hanyoyin samun makamashi da za su rage fitar hayaki mai gurbata muhalli.

Patricia Espinosa ta kuma bukaci gwamnatocin Afrika da su dauki matakan tinkarar sauyin yanayi, la'akari da yadda wasu bangarori da dama dake taimakon al'umma, da suka hada da na harkar gona da yawon bude ido da ruwa, ke gab da durkushewa saboda illolin sauyin yanayi.

Ta bayyana cewa, nahiyar na da kyawawan dabaru da suka hada da kara rungumar makamashi mai tsafta, wanda a yanzu ke taka rawa wajen rage tsadar samar da makamashi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China