Da yake jawabi yayin muhawarar kwamitin sulhu na majalisar ta kiran waya na bidiyo daga birnin Nouakchott na Mauritania, Moussa Mahamat ya ce bukaci a yi dukkan mai yuwa wajen kare hadin kan kasashe.
Ya ce shirin wanzar da zaman lafiya na MDD wani tubali ne na kasashen duniya na inganta tsaro da zaman lafiya, kuma alama ce dake nuna yadda ake martaba hadin kai da goyon bayan juna a duniya.
Ya ce Afrika ta dauki batun hadin kai da muhimmanci, inda ta dauke shi a matsayin hanya mai dorewa ta magance kalubalen tsaro da zaman lafiya. (Fa'iza Mustapha)