in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayyana kasashen Afrika a matsayin wadanda za su fi fuskantar barazanar kutsen intanet
2018-03-30 10:03:30 cri
Masana kan fasahar sadarwa ta zamani sun yi gargadin cewa, kasashen Afrika su ne suka fi fuskantar hadarin kutsen intanet saboda rashin kwarewarsu na tunkarar irin matsalar.

Masanan sun bayyana haka ne yayin wani taro kan fasahar sadarwa ta Cloud da tsaro intanet na bana, a birnin Kigali na Rwanda, inda taron na yini biyu ya mai da hankali kan bayyana rawar da tsaron intanet zai taka a matsayin jigo wajen samar da sabbin hanyoyin kasuwanci a yankin.

Ya kuma samar da wani dandali na tattaunawa tsakanin kwararru dake kokarin amfani da fasahar zamani wajen bunkasa tattalin arzikin yankin.

A cewar rahoton da hukumar kula da tattalin arziki ta duniya WEF ta fitar kan barazanar da za a iya fuskanta a duniya bana, a yanzu, ana ganin kutsen intanet a matsayin babbar barazana ta uku, bayan matsanancin rashin kyan yanayi da kuma iftil'i daga Allah.

A cewar kididdigar tsaron intanet na kungiyar kamfanonin sadarwar ta duniya na 2017, jajircewar kasashen Afrika wajen tsaron intanet shi a mataki mafi kasa, idan aka kwatanta da sauran nahiyoyi. Inda ta ce kasashen Mauritius da Masar ne kadai ke kan gaba a kokarin tsaron intanet a nahiyar.

Taron na bana ya ja hankalin sama da mahalarta 100 ciki har da kwarraru kan fasahar tsaron intanet da jami'an gwamnatoci da jami'ai daga bangarori masu zaman kansu daga yankin gabashin Afrika da sauran wurare. (Fa'iza Msuatpha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China