in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci nahiyar Afrika ta rungumi shuke-shuken gargajiya don magance matsalar sauyin yanayi
2018-04-10 10:12:42 cri

Hukumar MDD mai kula da harkokin samar da abinci da aikin gona FAO, ta yi kira ga kasashen Afrika su rungumi noman kayayyakin gargajiya domin magance matsalar sauyin yanayi.

Shugaban sashen shuke-shuke na hukumar Wilson Ronno, ya shaidawa wani taron manema labarai a Nairobin Kenya cewa, bincike ya nuna cewa kasashen kudu da hamadar sahara za su rasa wasu yankuna masu albarkar noma cikin gomman shekaru masu zuwa saboda sauyin yanayi.

Wilson Ronno wanda ya bayyana haka a jiya, lokacin da jami'an hukumar suka kai ziyara ofisoshin bincike kan harkokin gona da dabbobin gida na Kenya, ya ce ya kamata kasashen nahiyar su rungumi shuke-shuke irin na su dawa da gero da rogo da kayayyakin lambu da aka saba shukawa, domin za su taimakawa nahiyar yaki da sauyin yanayi saboda su na jure fari.

Jami'an hukumar a yanzu na ziyarar ayyukan da Kenya ke yi, wadanda suka samu tallafi daga asusun tallafawa harkokin gona na hukumar, wanda ke da nufin kara adadin shuke shuke masu gina jiki da manoma ke shukawa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China