in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban WTO ya lashi takobin mara baya ga yankin ciniki mara shinge na nahiyar Afrika
2018-04-04 10:54:16 cri
Darakta Janar na hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO Roberto Azevedo, ya lashi takobin mara baya ga shirin nahiyar Afrika na samar da yankin ciniki cikin 'yanci.

Da kamfanin dillancin labarai na Lusa Portuguese ya yi masa tambaya kan ko shirin na Afrika zai saba da manufofin WTO,Azevedo wanda ke Lisbon, ya ce ko kadan shirin ba zai sabawa manufofin hukumar WTO ba, inda ya ce dole ne WTO ta mara baya ga tsarin hadin kan Afrika.

Ya kara da cewa, wajibi ne dokokin hukumar su bada kulawa ta musamman ga hadin kai da ci gaban Afrika, wanda da ke da muhimmanci ga kasashen nahiyar, yana mai cewa za su yi dukkan mai yuwuwa wajen taimakawa shirin.

A cikin watan da ya gabata ne Shugabannin kasashen Afrika suka hadu a Rwanda, inda suka tattauana game da yankin ciniki mara shinge na nahiyar, yankin da zai kunshi dukkan kasashen Tarayyar Afrika 55.

Daga cikin kasashen 55, 44 ne suka rattaba hannu kan shirin a ranar 21 ga watan Maris, Yayin da sauran, musammam ma Nijeriya da tafi kowacce kasa a nahiyar yawan al'umma, ta nemi karin lokaci don nazirin shirin.

Idan shirin ya tabbata, zai samar da yankin ciniki cikin 'yanci mafi girma ta fuskar yawan kasashe mambobi, baya ga hukumar WTO dake da kasashe mambobi 164, ciki har da galibin kasashen Afrika. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China