in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kasuwar Sudan ta kudu zasu halarci baje kolin kasar Sin
2018-01-26 10:28:53 cri
Wani jami'in kasar Sin ya bayyana cewa kasar ta baiwa 'yan kasuwar Sudan ta kudu damammaki na halartar bikin baje kolin kayayyaki na kasa da kasa na kasar Sin irinsa na farko.

Zhang Yi, jami'in kula da harkokin tattalin arziki a ofishin jakadancin kasar Sin dake Sudan ta kudu ya bayyana cewa, kasar Sin zata dauki nauyin tawagar wakilan 'yan kasuwar na Sudan ta kudu da za su ziyarci kasar ta Sin.

Zhang ya ce, wannan yunkuri zai baiwa 'yan kasuwar Sudan ta kudun damar baje kolin hajojinsu kuma zai ba su kwarin gwiwa na samar da kayayyaki a cikin gida da kuma cigaban masana'antu a Sudan ta kudun.

Ministan ciniki na Sudan ta kudun Moses Hassan Tiel, ya bayyana kasar Sin cewa ta kasance babbar abokiyar kasuwancin kasar ta gabashin Afrika, tun bayan da kasar ta samu 'yancin gashin kanta daga kasar Sudan a shekarar 2011.

Ya ce baje kolin zai baiwa Sudan ta kudu kwarin gwiwa na samar da kayayyaki wanda hakan zai kara fadada harkokin kasuwanci tsakanin bangarorin biyu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China