in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta bunkasa shirin kiwon lafiya ta hanyar intanet
2018-04-13 10:43:11 cri

A kokarin da take yi na bunkasa tsarin kiwon lafiya ta hanyar fasahohin zamani wato Internet Plus healthcare, kasar Sin za ta yiwa cibiyoyin kiwon lafiyar kasar kaimi wajen yin amfani da tsarin kiwon lafiya ta hanyar intanet.

A wata sanarwar da aka fitar bayan kammala taron majalisar harkokin mulkin ta kasar wanda firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jagoranta jiya Alhamis, an ce, za'a baiwa cibiyoyin kiwon lafiyar kasar damar yin amfani da shafukan yanar gizo wajen bincika masu fama da cutuka ga mutane dake fama da cutuka masu wahalar magani, inda marasa lafiyar za su dinga ziyartar likitocinsu ta hanyoyin shafukan intanet.

Ana karfafa gwiwa ga tsarin asibitocin kasar biyu daga cikin uku na matakan kiwon kafiya a kasar, da su samar da tsarin kiwo lafiya ta hanyoyin intanet, da suka hada da mika bukatar ganin likita da duba sakamakon gwaje-gwaje.

Mista Li ya ce, "bunkasuwar tsarin kiwon lafiya na Internet Plus Healthcare, wani muhimmin shiri ne da zai kyautata sha'anin kiwon lafiya a kasarmu. Kuma zai kara taimakawa wajen bunkasuwar fannin tattalin arziki da cigaban zamantakewar jama'ar kasar."

"A yayin da kasar Sin ta shiga sahun jerin kasashen duniya masu matsakaicin cigaba wajen samun kudaden shiga, an samu matukar karin bukatun kiwon lafiya a kasar. Tsarin na Internet Plus Healthcare, zai taimaka wajen kawar da matsalolin rashin samun damammaki da rage tsadar kudaden kula da lafiya, wanda ya kasance batu da ya jima yana damun al'umma baki daya", in ji Li.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China