in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bill Gates: Cigaban fasahar kasar Sin zai bada gagarumar gudunmowa ga cigaban kiwon lafiya a duniya
2018-02-14 11:14:40 cri

Kasar Sin ta taba zama daya daga cikin kasashen dake amsar tallafin hukumomin kasa da kasa, amma a halin yanzu, ta kasance kasar dake sahun gaba a duniya wajen bada gudunmowa ga cigaban harkokin kudade da fasaha ga shirin kula da lafiya na duniya.

Attajirin nan da ya fi kowa kudi a duniya Bill Gates, ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua jiya Talata, inda ya furta cewa, kasar Sin ta yi matukar taka rawar gani wajen taimakawa wajen cike gibin dake akwai a shirin kiwon lafiya da kuma yaki da talauci a wasu gomman shekaru da suka gabata. Ya ce abin da ake fatan gani a halin yanzu shi ne, ba wai kawai kasar Sin ta yi amfani da fashar kirkire-kirkirenta wajen cigaba da taimakawa bukatunta na cikin gida ba ne, har ma ana fatan za ta yi amfani da su wajen taimakawa kasashe masu tasowa.

Gates, wanda ke jagorantar gidauniyar tallafi ta Bill da Melinda Gates Foundation, ya ce ya ga irin nasarar da kasar Sin ta samu wajen yin hadin gwiwa da gidauniyar wajen warware matsalar cigaban kiwon lafiya na cikin gida da kalubalolin cigaba a wasu gomman shekaru da suka shude.

A shekarar 2009, gidauniyar ta Gates Foundation, ta yi hadin gwiwa da kasar Sin wajen kaddamar da shirin hadin gwiwa na yaki da cutar tarin (TB), inda aka yi amfani da shirin a matsayin abin koyi don taimakawa kasar Sin wajen rage yawan mutanen da suke fama da cutar tarin TB, musamman wajen samar da magunguna masu yawa da za su iya kashe kaifin cutar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China