Jami'in hukumar Hou Yan, ya ce Kasar Sin za ta ci gaba da kokarin hada kamfanonin dake ayyukan kiwon lafiya da kamfanonin kula da tsoffi da na Yawon bude ido da motsa jiki da kuma na samar da abinci, ya na mai cewa a bara, kasar na fitar da kayayyakin aikin lafiya zuwa kasashe da yankuna 224.
A watan Octoban 2016 ne hukumomin kasar Sin suka fitar da wani jadawali da aka yi wa lakabi da 'Healthy China 2030' wanda ya kunshi bangarori kamar na kula da lafiyar al'umma da kamfanonin kiwon lafiya da na ingancin abinci da maganunguna, da nufin inganta lafiyar Sinawa. (Fa'iza Mustapha)