Hukumar kula da nakasassu ta kasar Sin a ranar Litinin ta sanar cewa, za'a gudanar da bikin baje kolin ne tsakanin ranakun 13 zuwa 15 ga watan Satumba, kuma kamfanoni da kungiyoyi kimanin 300 da suka fito daga kasashe 22 a sassa daban daban na duniya ne za su halarta.
A cewar Hu Xiangyang, daraktan sashen kula da harkokin samun sauki na hukumar din ya ce, 'yan kasuwa daga kasashe da kuma shiyyoyi dake kan hanyar ziri daya da hanya daya za su tattauna game da batun hadin kai.
Kasar Sin tana da mutane masu fama da nakasa sama da miliyan 85, da kuma tsoffi sama da miliyan 40 wadan da ke bukatar na'urorin tallafawa lafiyarsu. (Ahmad)