in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An kaddamar da shirin karfafa tsarin lura da asibitocin hukuma
2017-07-26 13:54:28 cri
Majalissar zartaswar kasar Sin, ta fidda wasu ka'idoji na gudanar da garambawul ga asibitocin kasar, ta yadda tsarin gudanarwar su zai zamo na zamani.

Ka'idojin wadanda aka fitar a jiya Talata, na kunshe da kudurori na zahiri, bisa tsari na kimiyya, da ingantattun manufofin gudanarwa, da sanya ido, wanda zai dace da manufofin kasar nan da shekarar 2020.

Ana fatan sabbin ka'idojin raya ayyukan kula da lafiyar al'ummar Sinawan, za su maida hankali ga tabbatar da nasarar kare lafiyar al'umma, da tabbatar da cewa asibitoci na aiki ba tare da maida hankali ga neman riba ba, tare da cikakken tsarin gudanarwa na zamani.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China