in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude rumfunan zabe don zabar shugaban kasar Masar
2018-03-27 09:47:21 cri
A jiya Litinin aka bude rumfunan zabe domin jefa kuri'a a zaben shugaban kasar Masar, inda ake sa ran shugaban kasar mai ci Abdel Fattah al-Sisi zai lashe zaben cikin ruwan sanyi.

Da misalin karfe 9 na safiya agogon kasar wanda ya yi daidai da karfe 7 agogon GMT aka bude rumfunan zaben, a rana ta farko wanda za'a shafe kwanaki uku ana jefa kuri'a.

Akwai sama da mutane miliyan 59 wadanda suka cancanci kada kuri'a a zaben na Masar, daga cikin adadin mutanen kasar miliyan 104. A makon da ya gabata, Masar ta kammala shirye shiryen zabenta bayan da ta tusa keyar bakin hauren dake kasarta wadanda suka fito daga kasashen duniya akalla 124.

Akwai rumfunan zabe kimanin 13,706 a fadin kasar, kana akwai jami'ai kimanin 18,000 dake sanya ido a zaben wanda kungiyoyi a kalla 53 na cikin gida da wasu na kasashen waje 9 suke sanya ido a zaben, bugu da kari akwai 'yan jaridu na kasashen waje sama da 680 da suka halarci zaben na Masar.

Za'a sanar da sakamakon zaben a ranar 2 ga watan Afrilu, kamar yadda hukumar zaben kasar Masar din ta tabbatar da hakan. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China