in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasar Masar 4 da 'yan ta'adda 10 sun mutu a wata arangama a yankin Sinai
2018-03-05 09:51:26 cri
Rundunar sojojin kasar Masar ta sanar a jiya Lahadi cewa, dakarunta 4 sun mutu kana wasu 'yan ta'adda 10 su ma sun mutu a yayin wata arangama da suka yi a kokarin fatattakar 'yan ta'addan a arewacin lardin Sinai.

Wannan hari na daya daga cikin matakan da Masar ta kaddamar a kwanan nan mai taken "Sinai 2018" na yunkurin kakkabe ayyukan ta'addanci, inda aka yi nasarar hallaka 'yan ta'adda 105, da kama wasu mutanen 3,200 wanda ake zarginsu da alaka da ta'addanci, sai dai an sake fiye da rabin mutanen bayan gudanar da bincike kansu, kana an samu nasarar tarwatsa maboyar 'yan ta'adda da wuraren da suke ajiye makamai sama da 1,400 tun daga lokacin da aka kaddamar da fara shirin a ranar 9 ga watan Fabrairu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China