in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta musanta rahoton yin garkuwa da jami'in diplomasiyyar Masar a Tripoli
2018-03-23 12:37:45 cri

A jiya Alhamis ma'aikatar harkokin wajen Libya ta musanta rahoto game da yin garkuwa da jami'in diplomasiyyar kasar Masar a babban birnin kasar Tripoli.

Wata sanarwa da ofishin ma'aikatar harkokin wajen kasar ya fitar ta musanta zargin da kafafen sada zumunta suka fitar dake nuna cewa, an yi garkuwa da jami'in diplomasiyyar na Masar, tana mai cewa, har ya zuwa yanzu jami'an ofishin jakadancin da karamin ofishin jakadancin kasar Masar din ba su koma bakin aiki ba a Tripoli.

Babban sashen dake kula da harkokin diplomasiyya da tsaro ya bayyana cewa, dukkannin labaran da shafukan sada zumunta na zamani suka watsa ba gaskiya ba ne, kuma dukkannin ofisoshin jakadanci suna karkashin kulawar jami'an tsaro ne.

Sashen ya kuma tabbatar da cewa, babu wani jami'in diplomasiyyar Masar dake zaune a Tripoli a halin yanzu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China