in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al Sisi ya sanar da halartar zaben shugaban kasar Masar da za a gudanar a shekarar 2018
2018-01-20 13:12:13 cri
Shugaban kasar Masar Abdelfattah al Sisi ya bayyana a jiya Juma'a cewa, zai tsaya takara a zaben shugaban kasar Masar da za a gudanar a watan Maris na bana.

Al Sisi ya sanar da wannan kuduri ne a gun taron manema labaran kasar Masar da aka gudanar a birnin Alkahira, inda aka bayyana irin nasarorin da aka samu yayin wa'adin shugaba Al Sisi na shekaru 4 na wannan karo. Al Sisi ya bayyana cewa, za a tabbatar da gudanar da zaben cikin tsari mai kyau, an kuma yi kira ga jama'a da su fita don jefa kuri'unsu a zaben.

Tun da farko dai hukumar zaben kasar Masar ta sanar da cewa, za a gudanar da zaben shugaban kasar Masar ne daga ranar 26 zuwa 28 ga watan Maris na shekarar 2018. Idan ba'a samu dan takarar da ya samu fiye da kahi hamshin na kuri'un zaben a zagayen farko ba, za a je zagaye na biyu. Za kuma a gabatar da sakamakon zaben na karshe ne a ranar 1 ga watan Mayu. Masu sha'awar takara za su yi rajistar shiga zaben tun daga ranar 20 zuwa 29 ga wannan watan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China