in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya yi kira da a samar da al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama
2018-04-10 10:46:43 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga jama'a a fadin duniya, da su yi aiki tare wajen samar da al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkan bil adama, tare da mayar da nahiyar Asiya da ma duniya baki daya wuri mai zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata da kuma ci gaba.

Shugaba Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabin bude taron shekara na dandalin Boao na nahiyar Asiya.

Ya ce da wannan buri a zuci, akwai bukatar girmamawa da daukar juna a matsayi guda.

Har ila yau, ya ce da wannan buri, akwai bukatar inganta tattaunawa da juna, da dauki nauyi tare, da hada hannu domin moriyar juna, da daukaka tsarin damawa da kowa, da neman kwanciyar hankali tare, da girmama sauran halittu, gami da kaunar duniyar da ake rayuwa cikinta. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China