Hada hadar cinikayyar kasar Sin da ketare yana samun karuwar kashi 14.5 bisa 100 na dalar Amurka, in ji shugaba Xi a jawabin da ya gabatar a lokacin bude taron dandalin Boao na Asiya na wannan shekara.
A cikin jawabin nasa shugaba Xi ya ce, al'ummar Sinawa sun samu ci gaba daga mataki mafi karancin karanci na tsawon rayuwa da kangin talauci, a halin yanzu, Sinawa suna cin moriyar albarkatu masu yawa da kuma samun rayuwa mai matsakaiciyar wadata.
A bisa ga alkaluman MDD na baya bayan nan, sama da al'ummar Sinawa miliyan 700 ne suka yi ban kwana daga kangin fatara, adadin da ya kai kashi 70 bisa 100 na adanin wadanda suka fita daga kangin fatara na duniya baki daya cikin wannan lokaci. (Ahmad Fagam)