in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Austria sun cimma matsayar kyautata alakar dake tsakaninsu
2018-04-09 09:38:56 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Austria Alexander Van der Bellen wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin sun cimma matsaya ta kafa kyakkyawar huldar abokantaka tsakanin kasashen na Sin da Austria ya zuwa matsayin dangantakar koli.

Van der Bellen wanda ya amsa goron gayyatar shugaba Xi, ya jagoranci babbar tawagar jami'an gwamnatinsa zuwa ziyarar aiki a kasar Sin, daga cikin jami'an, akwai firayin ministan kasar Sebastian Kurz, da ministoci 4, da wasu manyan 'yan kasuwan kasar.

Xi ya ce, wannan ziyara ta kara bayyanawa a fili yadda shugaba Van der Bellen da gwamnatin kasar Austria suke ba da muhimmanci ga dangantakarsu da kasar Sin.

Inda ya bayyana kasar Austria a matsayin muhimmiyar abokiyar huldar kasar Sin a nahiyar Turai, Xi ya ce, sabuwar gwamnatin Austria ta nuna matsayinta na yin aiki tukuru wajen tabbatar da karfafuwar dangantaka tsakaninta da kasar Sin, da nuna goyon bayan shawarar ziri daya da hanya daya. Xi ya yi matukar nuna yabo kan wannan mataki.

A nasa bangaren, Van der Bellen ya ce, kasar Austria a shirye take ta kara karfafa dangantakarta da Sin a fannonin da suka hada da cinikayya, zuba jari, nazarin kimiyya, kare muhalli, samar da makamashi mai tsabta, da fannin wasanni da raya al'adu.

Austria tana fatan ganin dangantaka tsakaninta da kasar Sin tana kara samun kyautatuwa, kuma a shirye take ta dauki dukkan matakan da za su kara karfafa dangantaka tsakanin bangarorin biyu, in ji Van der Bellen.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China