in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya jadadda bukatar inganta salon shugabanci a duniya
2018-04-09 09:33:20 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana bukatar inganta tsarin shugabanci a duniya.

Xi Jinping, ya bayyana haka ne a jiya Lahadi, lokacin da yake ganawa da Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres dake ziyara a kasar Sin.

Shugaba Xi Jinping ya ce akwai matsaloli da dama da ake fuskanta a duniya, wanda ke da alaka da salo da iya shugabanci a duniya, inda ya ce akwai bukatar kara matse kaimi wajen inganta tsarin shugabanci domin magance wadancan kalubale.

Shugaban ya ce dole ne ci gaban da kasar Sin ke nema ya zama ingantacce, kuma ya kamata burin ci gaban da ta mai da hankali kan walwalar al'umma, ya zama mizanin auna ci gaba.

Ya ce manufar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa ita ce, tuntubar juna da hadin kai tsakanin dukkan kasashe, inda ya ce dole ne hadin kan ya fara tsakanin manyan kasashe.

Har ila yau, Xi Jinping ya ce a shirye kasar Sin take ta yayata damarmakin ci gaban da ta samu ga sauran kasashen duniya, amma kuma ba za ta taba tilasta amfani da tsarinta da akidoji a kan kowacce kasa ba.

A nasa bangaren, Antonio Guterres ya yi amana cewa, kasar Sin za ta yi kyakkyawan tasiri kan harkokin da suka shafi duniya a cikin wasu gomman shekaru masu zuwa. Ya ce a yanzu ana fuskantar matsalolin da suka shafi zaman lafiya da ci gaba, wadanda ke bukatar a warware su ta hanyar hadin kan kasashen duniya. Yana mai cewa ya kamata a karfafa tsarin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa.

Ya ce kasar Sin ta zaman wani ginshiki mai muhimmanci ga hadin kai tsakanin kasa da kasa, kana ta zama wani karfi mai aminci da ake matukar bukata, ga zaman lafiya da ci gaba a duniya. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China